Gida

ZamaniWeb.comZamaniWeb.com

Tsarin Tsare Sirri

Sabuntawa na karshe: 20 ga watan Oktoba, 2018.

ZamaniWeb ("mu", "na mu") mai aiki a shafin yanar gizon https://zamaniweb.com ("Manhajar")

Wannan shafin zai sanar da kai/ke tsare-tsaren mu ne a game da karba, da yin amfani, da kuma bayyana Bayanan-kai a yayin da ka/ki ke amfani da Manhajar mu.

Ba za mu yi amfani da bayanan-kan ka/ki ba ko bayyana shi ga wani mahaluki sai dai abin da mu ka sanar a cikin wannan Tsarin Tsare Sirrin.

Mu na amfani da bayanan-kan ka/ki domin samarwa da kuma bunkasa aikin manhajar. Yin amfani da manhajar na nuni da cewan an amince da yadda mu ke karba da kuma amfani da bayanan a bisa wannnan tsarin.

Karba Da Kuma Amfani Da Bayanai

Yayin amfani da manhajar, za mu iya neman ka/ki ba mu wasu bayanan-kan ka/ki wanda za mu iya amfani da su don tuntuba ko tantance ka/ki. Bayanan-kan, ba tare da iyakancewa ba, sun hada da sunan ka/ki, jinsi, ranar haihuwa, kasa, lamban waya, adireshin email, sauran bayanai ("Bayanan-kai").

Bayanan Shiga

Mu na karban bayanan da madubin yanar ka/ki ya turo a duk lokacin da ka/ki ka ziyarci manhajar mu ("Bayanan Shiga"). Wannan bayanan shiga zai iya hadawa da bayanai kaman na adireshin sadarwan intanet na kwamfutar ka/ki wato "Internet Protocol" ("IP"), samfurin madubin yana wato "browser version", shafukan da ka/kika ziyarta na manhajar mu, da lokacin ziyarar, da tsawon lokacin da ka/kika dauka a kan shafukan da sauran kididdiga.

Kalman-Sirri

A yayin yin rajista a shafin yanar gizon ZamaniWeb, wajibi ne mai amfani da manhajar ya/ta zabi/kirkiri Kalman Sirri. Mai amfani da manhajar ne ke da dukkan alhaki na tabbatar da tsaron kalman sirrin da ya/ta zaba. Kalman Sirrin shi ne kadai hanyar tabbatar da cewan ba wani ne ke kutse cikin taskan ba. Don haka ana shawartan dukkan masu amfani da manhajar ZamaniWeb da su kirkiri kalman sirri mai tsaurin tsaro. Mai amfani da manhajar ba shi/ta da ikon sanar da wani ko wasu kalman sirrin da ya/ta zaba kuma ba shi/ta da ikon yin amfani da kalman sirrin wasu masu amfani da manhajar. Wajibi ne mai amfani da manhajar ya/ta sanar da ZamaniWeb idan ya/ta na zargin cewan wasu masu amfani da manhajar sun yi amfani da kalman sirrin shi/ta.

Masu Samar Da Aiyuka

Za mu iya daukan wasu kamfanoni ko mutane don gudanar da aikin manhajar mu, don gudanar da aikin a madadin mu, don gudanar da aiyukan da suka danganci aikin ko don taimaka mana wajen gane yadda ake amfani da manhajar mu.

Wadannan wasun na da daman riskan bayanan-kan ka/ki ne don gudanar da wadannan aiyuka a madadin mu kadai kuma an wajabta ma su da cewan kada su bayyana ko su yi amfani da shi don wani manufan na daban.

Tsaro

Tsaron bayanan-kan ka/ki ya na da muhimmanci a gare mu, sai dai a tuna da cewan babu wani hanyar sadarwa ta Intanet ko hanyar adana na lataroni wanda ya ke da tsaro na dari-bisa-dari. A yayin da mu ke kokari wajen yin amfaini da hanyar da aka amince da shi a kasuwance don tsare bayanan-kan ka/ki, ba za mu iya bayar da tabbaci na cikakken tsaron shi ba.

Mahadai Zuwa Wasu Shafukan

Manhajar mu zai iya kunsan mahadai zuwa wasu shafukan wadanda ba na mu ba. Idan ka/kika latsa mahadan shafukan wasu, mu na masu karfafa ba ka/ki shawara da cewan ka/ki duba Tsarin Tsare Sirri na kowane shafi da ka/kika ziyarta.

Ba mu da iko a kai, kuma ba mu da alhakin bayanan da tsare-tsaren tsare sirri ko aiyukan shafuka ko manhajar wasu.

Sirrin Yara

Manhajar mu ba ya bada gurbi ga mutane masu kasa da shekaru 13 ("Yara").

Ba mu karban bayanan-kai daga yara 'yan kasa da shekaru 13 a cikin sanin mu. Idan ku iyaye ne ko masu riko kuma kun san cewan yaron/yarinyar ku ya/ta bayyana bayanan-kai tare da mu, to a yi kokari a tuntube mu. Idan mu ka gano cewan yaro/yarinya mai kasa da shekaru 13 ya/ta bayyana bayanan-kai tare da mu, to za mu goge bayanan daga ma'adanar yanar gizon mu nan take.

Canje-canje Ga Wannan Tsarin Tsare Sirrin

Za mu iya sabunta Tsarin Tsare Sirrin mu daga lokaci zuwa lokaci. Za mu sanar da kai/ke duk wani canji ta hanyar sabuta wallafa Tsarin Tsare Sirrin a wannan shafin.

Mu na ba ka/ki shawara da cewan ka/ki rika duba wannnan Tsarin Tsare Sirrin a-kai-a-kai don sanin duk wasu canje-canje. Canje-canje ga wannan Tsarin Tsare Sirrin na fara aiki ne daga lokacin da mu ka wallafa shi a wannan shafin.

Tuntube Mu

Idan ka/ki na da wani tambaya game da wannan Tsarin Tsare Sirrin , to ka/ki tuntube mu.

Shawara: Ana iya latsa nan domin duba fassaran turanci (English) na wannan bayanin.