Gida

ZamaniWeb.comZamaniWeb.com

Game da Mu

ZamaniWeb.com manhajar yanargizo ne da ke bayar da daman kirkiran shafin yanargizo wato 'website' da kuma sarrafa shi cikin sauki, a harshen Hausa.

Muna alfahari da kasancewar ZamaniWeb shi ne manhajar gina shafin yanargizo na farko a Afrika. Kuma irin sa na farko a duniya wanda aka yi shi zalla cikin harshen Hausa.

Mun zabi yin wannan aiki cikin harshen Hausa ne kasancewar Hausa na daga cikin manyan yarurruka wanda ke da miliyoyin masu amfani da shi musamman a nahiyar mu ta Afrika.

Manufar Mu

Manufar mu shi ne samar da ingantacciyar hanya kuma mafi sauki na wallafa bayanai a intanet cikin harshen Hausa, ga masu amfani da harshen na Hausa da ke ko ina a fadin duniya.