Gida

ZamaniWeb.comZamaniWeb.com

Dokoki da Ka'idoji

Budo shafin yanar gizon da ke a https://zamaniweb.com ko kuma amfani da manhajar na nuni da cewa ka/kin amince da wadannan dokoki da ka'idojin kuma ka/kin amince da bin dukkanin dokokin da yankin ka/ki ta tanada. Idan ba ka/ki amince da dokoki da ka'idojin nan ba, to ba ka/ki da daman yin amfani da wannan manhaja na ZamaniWeb kuma ya wajaba ka/ki bar shafin ZamaniWeb nan take. Idan ana so a zama mamba a ZamaniWeb to dole ne a karanta wadannan dokoki da ka'idojin kuma a kiyaye su sannan a tabbatar mana da yin hakan a yayin yin rajista.

1. Mutanen da shekarun su ya haura 13 ne kadai ke da daman amfani da aiyukan manhajar ZamaniWeb. Mu na da daman cire mutum daga cikin masu amfani da manhajar ba tare da sanarwa ba idan muka gano ko aka sanar da mu ko kuma muna shakka cewan shekarun mai amfani da manhajar kasa da 13 ne.

2. A yayin yin rajista a shafin yanar gizon ZamaniWeb, wajibi ne mai amfani da manhajar ya/ta zabi kalman sirri. Mai amfani da manhajar ne ke da dukkanin alhakin tabbatar da tsaron kalman sirrin da ya/ta zaba. Mai amfaini da manhajar ba shi/ta da daman bayyana kalman sirrin ga wani ko wata ko wasu, ko kuma yin amfani da kalman sirrin wasu masu amfani da manhajar na ZamaniWeb. Wajibi ne mai amfaini da manhajar ya sanar da ZamaniWeb idan ya/ta na zargin cewan wasu masu amfani da manhajar na amfani da kalman sirrin shi/ta.

3. Mai amfani da manhajar ba shi/ta da daman daura wasu bayanai wadanda ya/ta saukar daga shafin yanar gizon ZamaniWeb zuwa wasu shafukan yanar gizon ko wallafa su ta kowace irin hanya.

4. Mai hakkin mallakan bayanan sa ne kadai ke da daman daurawa ko wallafawa a shafin yanar gizon ZamaniWeb. Matukar dai yin hakan ba zai sa ya/ta shiga hakkin wasu mutanen ba.

5. ZamaniWeb na da daman barin bayanan da mai amfani da manhajar ya daura har tsawaon wani lokaci, ko da mai amafani da manhajar ya daina amfani da manhajar.

6. Ga jerin misalan irin bayanai da fayilolin da aka haramta dorawa a manhajar ZamaniWeb:

7. Ga jerin misalan aiyukan da aka haramta yi a manhajar ZamaniWeb:

8. Mu na da daman cire duk wani bayani ko fayil ko kuma hana wallafa shi ba tare da sanarwa ko gargadi kafin yin hakan ba, idan muka fahimci cewan ya saba wa dokokin nan ko ya shiga hakkin wasu ko kuma ya saba wa dokokin Najeriya.

9. Wallafa bayanai a ZamaniWeb na nufin mai amfani da manhajar ya/ta fahimta kuma ya/ta amince cewan:

10. Ba lallai ne mu duba bayanan da mai amfani da manhajar ya dora ba. Idan mai amfani da manhajar na da shakku a kan ko bayanan da ya ke son dorawa sun saba wa dokokin nan ko basu saba ba, to mai amfani da manhajar ba shi da daman dora wadannan bayanan.

11. ZamaniWeb na iya canja wadannan dokokin a kowane lokaci ba tare da sanarwa ba. Ci gaba da amfani da manhajar ko shafin yanar gizon ZamaniWeb na nuni da cewan an amince da samfurin wadannan dokokin da ka'idojin mafi sabunta a wannan lokacin.

Shawara: Ana iya latsa nan domin duba fassaran turanci (English) na wannan bayanin.