Gida

ZamaniWeb.comZamaniWeb.com

Tambayoyin da aka fi yawan yi tare da amsoshin su

  1. Ina so in kirkiri website wato shafin yanar gizo a ZamaniWeb, ya ake yi?

    Sai ka fara yin rajistan taskan gudanar da aiyuka a ZamaniWeb, sannan sai ka shiga taskan, a nan ne za ka samu daman kirkiran shafin yanar gizon ka. Latsa nan don karanta cikakken bayani kan yadda za a kirkiri shafin yanar gizo a ZamaniWeb.

  2. Na yi rajista, na duba sakonnin Email din nawa amma ban ga sakon tantancewan ba, ya zan yi?

    Idan ba ka ga sakon a bangaren "Inbox" na Email din na ka ba, to ka duba bangaren "Spam" ko "Junk mails" na email din, domin zai iya yiwuwa ya fada a nan ne bisa kuskure. Idan kuma har ka duba nan din ba ka gani ba, to sai ka zo ka shiga taskan ka na ZamaniWeb (login) tare da lakabi da mabudin sirrin da ka yi rajistan, idan ka shiga za ka ga sanarwan da ke cewa "ba a tantance adireshin email ba" sannan a kasan shi za ka ga maballin da ke cewa "Sake aika sakon tantancewan!" to sai ka latsa wannan maballin na sake aika sakon tantancewan. Bayan haka sai ka sake komawa zuwa duba sakonnin email din ka, a nan za ka ga sakon tantancewan ya iso da yardan Allah. Idan kuma ka fahimci cewan sakon bai je ba ne saboda ka yi kuskure wajen rubuta adireshin email din tun a lokacin da ka yi rajista, to idan ka shiga taskan, za ka ga maballin da ke cewa "Gyara adireshin email" to sai ka latsa shi, zai budo maka shafin da za ka sabunta adireshin email din, sannan sai ka dawo baya ka latsa maballin "Sake aika sakon tabbacin" don samun sakon zuwa email din ka.

  3. Idan na yi gyara wato na sabunta saice-saicen shafi na sai in ga sabon saitin bai canjawa a nan take, mene ne matsalar?

    Wannan ba ya na nufin ba a adana sabon saitin da ka yi ba ne, a'a, mafi yawanci daga madubin yanar ka ne wato 'browser'. A duk lokacin da ka ga haka to kawai ka sake loda shafin, ma'ana ka latsa alaman 'refresh' na browser din ka domin sabunta budo shafin. Nan take za ka ga sabon saitin da ka yi ya bayyana.