Gida

ZamaniWeb.comZamaniWeb.com

Yadda Za a Kirkiri Sabon Shafin Yanar Gizo a ZamaniWeb Cikin Matakai 4

1

Yin Rajista (Bude Taska)

Idan wannan shi ne zuwan ka na farko, to dole ne sai ka yi rajista, wato sai ka mallaki taskan gudanar da aiyuka a ZamaniWeb. Yin rajistan har kirkiran shafi duk kyauta ne.

2

Tantance Adireshin Email

Domin kammala yin rajistan, za mu aika da sakon tantancewan zuwa ga adireshin Email din da aka yi rajistan da shi.

3

Shiga Taska

Shiga taskan ka na ZamaniWeb a ko da yaushe don gudanar da aiyukan shafin yanar gizon ka, ta hanyar amfani da kalman sirrin da ka yi rajistan da shi.

4

Kirkiran Shafin

Kirkiri shafukan yanar gizo har guda biyar a karkashin taskan ka na ZamaniWeb. Za a samu daman sarrafa kowanne shafin yanar gizo da aka kirkira a ko da yaushe.

1. Yin Rajista (Bude Sabon Taska)

Idan kai sabon zuwa ne, dole sai ka fara yin rajista na sabon taska wato "New Account Registration" kenan a turance. Yin rajistan sabon taskan kyauta ne kuma galibi bai wuce mintuna 2-3 ba. Ana yin rajistan ne ta hanyar shiga shafin yin rajistan, wato idan ka budo shafin farko na ZamaniWeb (zamaniweb.com) sai ka latsa maballin da ke cewa "Yi Rajista". Ko kuma kai tsaye, ana iya bin zamaniweb.com/administrator/shafin-rajista. A shafin yin rajistan za a ga fom mai guraben cikewa kamar haka:

 • Lakabi
 • Cikakken Suna
 • Jinsi
 • Kasa
 • Adireshin Email
 • Kalman Sirri
 • Maimaita kalman sirri

Mene ne Lakabi?
Lakabi shi ne wani dan gajeren taken da za a rika amfani da shi a duk lokacin da aka bukaci shiga cikin taskan ZamaniWeb don gudanar da harkokin shafi. Alamomin haruffa da lambobi da alaman jan layi ne kadai lakabi zai iya kunsa. Wajibi ne kada lakabin ya gaza alamomi 3 kuma kada ya zarce alamomi 20.

Mene ne Kalman Sirri?
Kalman sirrin ka shi ne mabudin sirrin ka. Shi ne wani dan kalma ko surkullen da za a yi amfani da shi a duk lokacin da aka bukaci shiga taskan ZamaniWeb don gudanar da harkokin shafi. Zai iya kasancewa wasu alamomi ne ko haruffa ko kalma ko lambobi wanda mutum shi kadai ya san abin sa kuma ba zai mance da su ba. Kada a kuskura a yi sakaci har wani ya san kalman sirrin don guje ma fadawa tarkon masu kutse da satan shafi. Wajibi ne kada kalman sirrin ya gaza alamomi 6.

Wajibi ne a cike kowane gurbi da ke fom din sannan a latsa maballin "Aika bukatan yin rajistan" da ke kasan fom din. Idan an samu nasaran yin rajistan, za a ga sakon "barka" ya bayyana a saman shafin wanda ke nuna cewa rajistan ya kammalu kuma sabon taskan ya budu. Daga nan sai a je zuwa mataki na gaba wanda shi ne tantance adireshin Email.

2. Tantance Adireshin Email

Wajibi ne sai mai rajista ya tantance adireshin Email din da ya yi rajistan da shi, ta hanyar latsa mahada ("link") da ke cikin sakon Email din da manhajar mu ya aika ma sa kai tsaye zuwa "Inbox" na adireshin Email din sa a lokacin da ya kammala cike fom na rajistan. Don haka bayan mutum ya kammala aika bukatan yin rajistan kaman yadda mu ka fado a mataki na farko, to sai ya je ya duba cikin sakonnin Email din sa, zai ga sabon sako daga ZamaniWeb, sai ya bude sakon, a cikin sakon zai ga mahadan tantancewan ("verification link") sai ya latsa shi. Idan ya latsa mahadan zai ga shafin ZamaniWeb ya budo tare da wani sanarwan da ke nuni da cewan an tantance adireshin Email din. Shi ke nan! Rajistan ya kammalu, daga nan zai iya shiga cikin taskan a ko da yaushe don gudanar da harkokin shafi.

3. Shiga Taska

Shiga cikin taska wanda a turance a kan ce "Account log in" ko "Sign in" shi zai ba ka daman cin moriyar dukkan bangarorin ZamaniWeb, kaman bangaren kirkiran sabon shafin yanar gizo da bangaren sarrafa shafukan yanar gizon da ka kirkira da dai sauran su. Domin shiga cikin taskan ka na ZamaniWeb a ko da yaushe sai ka latsa maballin "Shiga Taska" wanda ke shafin farko na ZamaniWeb ko kuma kai tsaye ana iya bin zamaniweb.com/administrator/shafin-shiga. A shafin shiga taskan za a ga wani dan gajeren fom mai guraben cikewa guda biyu kamar haka:

 • Lakabi
 • Kalman Sirri
Sai a rubuta lakabin da aka yi rajistan taskan da shi a gurbin lakabin. Sannan kuma a rubuta kalman sirrin da aka yi rajistan taskan da shi a gurbin kalman sirrin. Sannan sai a latsa maballin "Shiga da ni ciki" da ke kasan fom din.

4. Kirkiran Sabon Shafin Yanar Gizo

Bayan shiga taskan, kai tsaye, za a fado bangaren farko na "Taskar Mai Gudanarwa" wato "Administrator dashboard" kenan a turance. A nan ne za a samu daman kirkiran sabon shafin yanar gizo, da kuma daman shiga bangaren sarrafa shafukan yanar gizon. A shigowa na farko, za a ga wani sanarwa a sama mai nuni da cewan ba ka kirkiri wani shafi ba a halin yanzu, kuma idan ka yi, jerin shafukan da ka kirkira zai baiyana a nan. A kasa da wannan za a ga wani fom mai taken "Kirkiri Shafin Yanar gizon Ka" ko "Kirkiri Shafin Yanar gizon Ki". Wannan fom shi ne za a cike domin kirkiran sabon shafin yanar gizo a ZamaniWeb. Wannan fom na da guraben cikewa guda hudu kamar haka:

 • Taken Adireshin Shafin
 • Taken Shafin
 • Nau'in Shafin
 • Yaren Shafin

To a gurbi na farko, wato "Taken adireshin shafi" za ka rubuta kalma ne wanda ka ke son ya kasance a cikin adireshin shafin da za ka kirkira. Misali: Idan kana so taken adireshin ya kasance www{dot}wasanni{dot}zamaniweb{dot}com ne to sai ka rubuta "wasanni" a gurbin na taken adireshin shafin. Kalman kadai za ka rubuta. Idan ma sunan ka ka ke son ya fito a cikin taken adireshin, to sunan kadai za ka rubuta, misali "Adam". Ba a bada tazara wajen rubuta kalman na taken adireshin shafin kuma ba a sanya alamomin rubutu irin su aya da wakafi, amma za ka iya amfani da alaman "-" idan kana bukata. Kada kalman ya wuce guraben haruffa 20.

Sai gurbi na biyu, wato "Taken Shafi". Wannan shi ne ainahin sunan shafin ko kuma taken shafin. Za ka rubuta ainahin taken shafin ne ko kuma duk wani rubutu da ka ke son ya kasance a saman shafin da za ka kirkira. Taken shafin ka shi ne abu na farko da maziyarta shafin ka za su gani a saman shafin. Shi wannan "taken shafi" ba daya ya ke da "taken adireshin shafi" ba. Taken shafin zai iya kasancewa kalma daya ko kuma jerin kalmomi. Za ka iya amfani da alamomin rubutu kuma za ka iya bada tazara yayin rubuta taken shafin.

Gurbi na uku kuwa, wato "Nau'in Shafi" kana taba shi zai jero maka abubuwan zabi. Sai ka zabi nau'in shafin da ka ke son kirkira. Misali, idan shafin na kasuwanci ka ke son kirkira, to sai ka tabbatar ka zabi "Na kasuwanci" a nan wajen.

Gurbi na hudu kuma, wato "Yaren Shafi" shi ma da ka taba zai jero maka abubuwan zabi, sai ka zaba. Misali, idan shafin turanci ka ke son ka kirkira, to sai ka tabbatar ka zabi "English" a nan wajen.

Bayan haka sai a latsa maballin "Kirkiri Shafi" da ke kasa. Shi ke nan!