Gida

ZamaniWeb.comZamaniWeb.com

Bayan Na Kirkiri Sabon Shafin Yanar Gizo Na, Sai Kuma Me?

Bayan an kirkiri sabon shafin yanar gizo a ZamaniWeb, akwai wasu abubuwa guda 4 masu matukan muhimmanci a yi su, kamar haka:

(1) Gyara Bayanan Shafi

Abu na farko kuma mafi muhimmanci da ya kamata a gaggauta yi bayan an kirkiri sabon shafin, shi ne gyara bayanan shafin. Bayanan shafin su ne kaman haka:

Gargadi: A tabbata an latsa maballin "Sabunta bayanan" da ke kasa, bayan an kammala rubuta bayanan, domin adanawa.

Akwai kuma bangaren "Gyara Mahadan Shafukan Sadarwa" da ke kasa. Wanda shi kuma zai ba ka daman rubuta "@User-name" na ka na shafin zurukan zumunta wato na:

(2) Canja Hotunan Shafin

Abu na biyu da ya kamata a yi, bayan an sabunta bayanan shafin, shi ne canja hotunan shafin. A lokacin da ka kirkiri sabon shafin yanar gizon ka, idan ka ziyarci shafin za ka ga akwai wasu hotuna da muka saka a matsayin sumfur wato mun saka wadannan hotunan ne kawai domin mu nuna maka inda hotunan ka za su kasnace idan ka dora. Don haka sai ka je ka canja hotunan, ka dora naka hotunana wadanda suka danganci aiyukan shafin ka. Domin canja hotunan, sai ka shiga taskan ka, ka shiga sashin sarrafa shafin naka , sai ka latsa "Canja Hotunan Shafi". Idan daman nau'in shafin ka na kasuwanci ne ko na kungiya, to za ka ga hotuna hudu ne za ka bukaci canjawan kaman haka:

Yadda Ake Canja Hoton Bangon Shafi

Shi Hoton bango shi ne hoton da ke sama a shafin ka, kuma a kan sa ne taken shafin zai kasance. Domin canja hoton bangon, bayan ka budo bangaren "Canja Hotunan Shafi" za ka ga taken "Canja Hoton Bangon Shafi" a farko. Sannan za ka ga hoton da ke kai a halin yanzu. To kana da zabi guda biyu a nan:

Idan ka na so ka zabi hoton ne daga cikin jerin hotunan mu, to sai ka latsa wajen da aka ce "Zabi Hoto daga jerin hotunan mu" domin zaban hoton da ka ke so ya hau shafin ka a matsayin hoton bango.

Idan kuma ka na so ka dora na ka hoton ne wato "upload", sai ka yi kasa kadan za ka ga wajen da za ka taba don dauko hoto daga kwamfutar ka ko wayar ka, sai ka latsa "Dora hoton".

Gargadi: A tabbata cewa fadin hoton ya kasance tsakanin 820px zuwa 1500px. Sannan tsayin sa kuma kada ya zarce 600px.

Ana iya amfani da kowane "Image Editor" domin yin "resize" din hoton zuwa tsayin da kuma fadin da ake bukata kafin a dora.

Yadda Ake Canja Sauran Hotunan Shafin

Idan ka latsa "Canja Hotunan Shafi" bayan ya bude, sai ka yi kasa, wato ka wuce wajen canja hoton bango. Za ka ga inda aka sa taken "Canja Hoto na farko". Sannan za ka ga hoton da ke kai a halin yanzu. Sannan kuma za ka ga wajen da za ka taba don dauko hoto daga kwamfutar ka ko wayar ka , sannan ka latsa "Dora hoton".

Haka ma za ka yi domin canja hoto na biyu da na ukun.

(3) Canja Launin Shafi

Abu na uku da ya kamata a yi bayan kirkiran sabon shafi shi ne canja launin shafin wato "theme colour", idan ana bukata. A lokacin da ka kirkiri sabon shafin ka idan ka ziyarci shafin , za ka ga jimillan launin shafin shi ne baki ("black theme"). To za ka iya canja jimillan launin shafin zuwa kalan da ya dace da kasuwancin ka ko kalan kamfanin ka, cikin sauki ta hanyar zaba daga cikin jerin kalolin da muka tanadar. Domin canja launin shafin sai ka shiga taskan ka na ZamaniWeb, sai ka shiga sashin sarrafa shafin ka, sai ka latsa "Canja Launin Shafi". Idan ya budo, za ka ga jerin launuka, wato kalolin da za ka iya zaba. Sai ka zabi kalan da ka ke so ta hanyar latsa shi, sannan sai ka yi kasa, ka latsa maballin "Sabunta Saitin Launin".

(4) Canja Saice-saicen Shafi

Abu na hudu mafi muhimmanci da ya kamata a yi bayan kirkiran sabon shafi shi ne canja saice-saicen shafin idan ana bukata. Saice-saicen shafin wanda za a gani idan aka latsa "Canja Saice-saicen shafi" su ne kaman haka:

Bayan an kammala zaban saice-saicen, sai a latsa maballin "Sabunta Saitin" da ke kasa.