ZamaniWeb - Shafin farko
Barka Da Zuwa ZamaniWeb.com
Barka Da Zuwa ZamaniWeb.com

Sabuwar fasahar kirkiran shafin yanar gizo da ke bai wa kowa daman mallakan tsararren shafin yanar gizo cikin mintuna 5, a harshen Hausa.

Yi Rajista Yi Rajista Shiga Ciki Shiga Ciki
+234 (0) 9046071870
ZamaniWeb.com manhajar yanar gizo ne da ke bayar da daman kirkiran shafin yanar gizo da kuma sarrafa shi cikin sauki, a harshen Hausa. Yanzu za ku iya mallakan shafin yanar gizon ku don amfanin al'ummar ku ko kuma don bunkasa harkokin kasuwancin ku a zamanance.

ZamaniWeb shi ne manhajar yanar gizo irin sa na farko a duniya wanda ya fito da sabuwar hanyar mallakan shafin yanar gizo a harshen Hausa. Burin mu shi ne mu baka daman mallakan shafin yanar gizo a yanzu-yanzun nan, a kyauta, kuma a saukake.

Da zaran ka kaddamar da shafin yanar gizon ka a ZamaniWeb.com kai tsaye manhajar mu zai kirkiri adireshin shafin ka mai saukin fade da yadawa kaman: www.takenshafin.zamaniweb.com Don haka nan take kowa zai iya ziyartan sabon shafin ka!

1 / 6
Bude katafaren shafin ku na yanar gizo wanda aka
tsara shi a zamanance cikin harshen Hausa!
2 / 6
Za ku samu adireshin shafin yanar gizo na musamman
wanda mutane za su rika bi domin su ziyarci shafin ku, a kyauta!
3 / 6
Adireshin shafin ku zai kasance kamar haka:
www.takenshafin.zamaniweb.com
4 / 6
Samu tsararren shafin yanar gizon ku mai kyawun budowa
har a kan manya da kananan wayoyin hannu!
5 / 6
Bunkasa harkokin kasuwancin ku a zamanance kuma a hausance,
ta hanyar shafin ku na yanar gizo, don samun riba mai yawa.
6 / 6
Dora dukkanin bayanai ko kuma fayilolin da kake bukata
a shafin yanar gizon ka na ZamaniWeb!

Ya Manhajar ZamaniWeb Ya ke?

Ga kadan daga cikin abubuwan da za ku samu tare da manhajar yanargizon ZamaniWeb.com:

Shafi mai kyawun gani a duk nau'ukan kwamfuta da wayoyi.

Adireshi mai saukin fade kaman www.takenshafin.zamaniweb.com.

Daman yin saice-saice da canja fasali da launin shafi.

Daman wallafa bayanai zuwa shafin ka cikin sauki.

Daman dora nau'ukan daban-daban na fayiloli a shafin ka.


< ha >

Daman kirkiran shafukan yanargizo a harshen Hausa da turanci.

Daman kasancewa a shafukan bincike-bincike musamman Google.


₦0.00

Daman samun tsararren shafin yanargizo na kyauta.

Manufar Mu

Manufar mu shi ne samar da ingantacciyar hanya kuma mafi sauki na wallafa bayanai a intanet cikin harshen Hausa, ga masu amfani da harshen na Hausa da ke ko ina a fadin duniya.

Biyo mu a: Facebook twitter Instagram

Kana da bayanan da kake son watsawa a intanet?

Wallafa kasidu da hotunan ku ko sautuka da bidiyoyi a duniyar intanet ya zama abu mai sauki ta hanyar ZamaniWeb. Kirkiri shafin ku yanzu domin isar da sakonnin ku, manufofin ku da bayanan aiyukan ku ga dimbin al'umma da ke ko ina a fadin duniya, a hausance kuma a zamanance!

Kai dan kasuwa ne, ko mai sana'ar hannu?

Komai girma ko kankantar sana'ar ka ko kasuwancin ka ko kamfanin ka, za ka iya mallakan matsakaicin shafin yanar gizon ka a ZamaniWeb, wanda zai ishe ka bunkasa harkokin cinikayyan ka da kuma sadarwa tsakanin ka da abokan cinikayyan ka na nesa da na kusa, a saukake kuma a zamanance!

Hanya mafi sauki da sakon ka zai riski dimbin jama'a!

Kasancewar yawaitar masu amfani da fasahar intanet karuwa ya ke yi a kullum musamman ma ta wayoyin hannu, shafin yanar gizo shi ne hanya mafi sauki da bayanan ku za su riski dimbin jama'a da ke ko ina a fadin duniyar nan. Bude sabon shafin ku yanzu domin fara wallafa bayanan ku a intanet cikin sauki.

614+
Na adadin shafukan da aka kirkira
1572+
Na adadin mutanen da suka yi rajista
646+
Na kasidun blog da aka wallafa
1210+
Na sharhi a kan kasidun blog

Shin me za ku tsaya jira?

Kirkiri Shafin Ku Yanzu! Kirkiri Shafin Ku Yanzu!