Mene ne ZamaniWeb?
ZamaniWeb.com manhajar yanargizo ne da ke bayar da daman kirkiran shafin yanar gizo da kuma sarrafa shi cikin sauki, a harshen Hausa.
Yanzu za ku iya mallakan shafin yanargizon ku don amfanin al'ummar ku ko kuma don bunkasa harkokin kasuwancin ku a zamanance. Burin mu shi ne mu baka daman mallakan shafin yanargizo a yanzu-yanzun nan, a kyauta, kuma a saukake.
Da zaran ka kaddamar da shafin yanargizon ka a ZamaniWeb.com kai tsaye manhajar mu zai kirkiri adireshin shafin ka mai saukin fade da yadawa kaman: www.takenshafin.zamaniweb.com Don haka nan take kowa zai iya ziyartan sabon shafin ka!
Ko kun san muhimmancin mallakan shafin yanargizo?
Sama da mutane Biliyan 4 ne ke amfani da intanet a kullum
Kasancewar yawaitar masu amfani da intanet musamman ma ta wayoyin hannu, shafin yanargizo shi ne hanya mafi sauki da bayanan ku za su riski dimbin jama'a da ke ko ina a fadin duniya.
Bude katafaren shafin ku ko blog, domin fara wallafa labaran ku cikin sauki. Babu bukatar sai kun nemi kwararre wajen bude shafin ku. Gina shafin yanargizo babu wahala a ZamaniWeb. Domin ana iya kirkira da kuma sarrafa shafuka cikin sauki daga kowace irin wayar hannu.
Bunkasa alakar kasuwanci da abokan cinikayya
Abokan cinikayyar ku za su samu daman aiko maku da sakonnin su ta hanyar cike fom a shafin ku.
Dora Hotuna da Sautuka da Bidiyoyi
Wallafa rubuce-rubuce da hotuna da sautuka da bidiyoyi a shafin yanargizon ku don amfanin jama'ar ku.
Tallata manufofin ku
Yi amfani da shafin yanargizon ku don kayatarwa da janyo ra'ayin abokan huldar ku.
Da me manhajar ZamaniWeb yai fice?
Ga kadan daga cikin abubuwan:
Shafi mai kyau
Kyawun budowa a kowane kwamfuta da wayar hannu.
Saukin Sarrafawa
Saukin yin saice-saice da canja fasali da launin shafi.
Saukin Wallafa Bayanai
Saukin wallafa rubuce-rubuce zuwa shafin ka.
Shafi a Harshen Hausa
kirkiran shafukan yanargizo a harshen Hausa da turanci.
Kasancewa a Google
Fitowa a shafukan bincike-bincike musamman Google.
Shafi a Kyauta
Daman samun tsararren shafin yanargizo a kyauta.
Na adadin shafukan da aka kirkira
Na adadin masu rajista
Na kasidun blog da aka wallafa
Na sharhi a kan kasidun blog
Tambayoyi Da Amsoshi
Ga amsoshin wasu tambayoyin da muka fi yawan samu:
-
Ina so in kirkiri website wato shafin yanargizo a ZamaniWeb, ya ake yi?
Sai ka fara yin rajistan taskan gudanar da aiyuka a ZamaniWeb, sannan sai ka shiga cikin taskan, a nan ne za ka samu daman kirkiran shafin yanargizon ka. Latsa nan don karanta cikakken bayani kan yadda za a kirkiri shafin yanargizo a ZamaniWeb
-
Wasu matakai ake bi kafin a mallaki shafin yanargizo a ZamaniWeb?
Matakai guda hudu ne masu sauki kamar haka:
(1) Yin Rajista (Bude sabon taska a ZamaniWeb)
(2) Tantance Adireshin Email
(3) Shiga Ciki (shiga cikin taskan da aka yi rajista)
(4) Kirkiran shafi
-
Nawa zan tanada kafin in mallaki shafin yanargizo na a ZamaniWeb?
Yin rajista har kirkiran shafin duk kyauta ne a ZamaniWeb. Babu bukatar biyan ko sisi. Amfani da dukkan kayan aiyukan da ke manhajar ZamaniWeb kyauta ne. Saidai bayan kirkiran shafin ka, za ka iya biya don samun wasu karin aiyuka na musamman a shafin ka, a duk lokacin da ka so yin hakan. Muna da tsarukan da za su dace da dukkanin abubuwan da kake bukatan samu a shafin ka. Duba Shafin farashi da tsare-tsaren mu don karin bayani.
-
Mene ne Lakabi da Kalman Sirri??
Lakabi shi ne wani dan gajeren taken da za a rika amfani da shi a duk lokacin da aka bukaci shiga cikin taskan ZamaniWeb don gudanar da harkokin shafi. Ana zaban lakabin ne a yayin yin rajista a ZamaniWeb. Dole ne lakabin ya kasance kalma guda daya. Alamomin haruffa da lambobi da alaman jan layi ne kadai lakabi zai iya kunsa. Sannan wajibi ne kada lakabin ya gaza alamomi 3 kuma kada ya zarce alamomi 20.
Shi kuma Kalman sirrin ka shi ne mabudin sirrin ka. Shi ne wani dan kalma ko surkullen da za a yi amfani da shi a duk lokacin da aka bukaci shiga taskan ZamaniWeb don gudanar da harkokin shafi. Ana zaban kalman sirrin ne a yayin yin rajista a ZamaniWeb. Zai iya kasancewa wasu alamomi ne ko haruffa ko kalma ko lambobi wanda mutum shi kadai ya san abin sa kuma ba zai mance da su ba. Kada a kuskura a yi sakaci har wani ya san kalman sirrin don guje ma fadawa tarkon masu kutse da satan shafi. Sannan wajibi ne kada kalman sirrin ya gaza alamomi 6. -
Na yi rajista, na duba sakonnin Email din nawa amma ban ga sakon tantancewan ba, ya zan yi?
Idan ba ka ga sakon a bangaren "Inbox" na Email din na ka ba, to ka duba bangaren "Spam" ko "Junk mails" na email din. Idan kuma har ka duba nan din ba ka gani ba, to sai ka zo ka shiga cikin taskan ka na ZamaniWeb tare da lakabi da kalman sirrin da ka yi rajistan da su. Idan ka shiga za ka ga sanarwan da ke cewa "ba a tantance adireshin email ba" sannan a kasan shi za ka ga maballin da ke cewa "Sake aika sakon tantancewan!" to sai ka latsa shi. Bayan haka sai ka sake komawa zuwa duba sakonnin email din ka, a nan za ka ga sakon tantancewan ya iso da yardan Allah. Idan kuma ka fahimci cewan sakon bai je ba ne saboda ka yi kuskure wajen rubuta adireshin email din tun a wajen yin rajista, to duk dai idan ka shiga cikin taskan, za ka ga maballin da ke cewa "Gyara adireshin email" to sai ka latsa shi, zai budo maka shafin da za ka sabunta adireshin email din, sannan sai ka dawo baya ka latsa maballin "Sake aika sakon tantancewan" don samun sakon zuwa email din ka.
-
A ina zan samu karin bayanai da amsoshin wasu tambayoyin game da ZamaniWeb?
Domin samun dukkanin bayanan taimako game da ZamaniWeb sai a shiga shafin mu na: Bayanan Taimako